fbpx
Thursday, February 25
Shadow

An kama wani Mutum da ya lallaba gidan wata mata ya sumbaceta tana bacci

An kama wani mutum me shekaru 33 da ya lallaba gidan wata mata ya sumbaceta sau da dama a yayin da take bacci.

 

Mutumin da yayi aika-aikar ne ya mira ‘yansanda da misalin karge 12 na yamma yana korafin cewa wasu na aon su ji masa.

 

Da yansandan suka je, sun tarar da wasu mutane a tsaye a kofar dakin mutumin inda shi kuma ya kulle kansa a ciki. Rahoton yace matar ta tashi ta ga mutumin na sumbatarta inda ta kwarma ihu, shine ya gudu.

 

Jami’an tsaron sun kwashe kusan awanni 2 suna fama dashi ya bude kofar inda daga baya dai ya bude kuma aka kamashi. Lamarin ya farune a kasar Singapore kamar yanda kamar yanda Newsnow ta UK ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *