fbpx
Friday, February 26
Shadow

An kama wani mutum mai shekaru 30 bisa zargin yiwa wata yarinya ‘yar shekaru 12 fyade a Jihar Nasarawa

Jami’an tsaro masu baiwa farar hula kariya (Civil Defense) sun cafke wani matashi mai shekaru 30, Mohammed Sani, bisa zargin lalata wata yarinya ‘yar shekara 12 a yankin Angwatashi da ke karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

Da yake gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai a hedikwatar NSCDC da ke Lafia, babban birnin jihar, a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu, kakakin rundunar, Saraju Muhammed, ya ce Mohammed ya yaudari yarinyar ne zuwa wani kebantaccen wuri da sunan zai sayi ruwan sha a wurinta, sannan yayi mata fyade.

Asirin wanda ake zargin ya tonu ne bayan wanda aka wa fyaden ta koma gida kuma iyayenta sun lura da yanayin da take ciki.

Bayan sun tambaye ta, ta fada wa iyayenta yadda wanda ake zargin ya yi mata fyade, ta ce wanda ake zargin ya yi mata barazanar kashe ta idan har ta bayyana abin da ya yi mata.

Ba tare da bata lokaci ba iyayenta suka kai rahoton faruwar lamarin ofishin ‘yan sanda na Angwatashi kuma an kama wanda ake zargin.

Suraju Muhammed ya ce tuni wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, kuma za a gurfanar da shi a kotu da zaran an kammala bincike a kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *