Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas sun cafke wani shahararren shugaban kungiyar asiri ta Aiye, Segun Ezekiel, bisa zargin kashe abokin hamayyar kungiyar Eiye a yankin Bariga na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Muyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar da cafke shugaban kungiyar ta sirrin a wata sanarwa a ranar Asabar, 3 ga Afrilu, ya ce wanda ake zargin ya kasance yana addabar dukkan yankin Bariga.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ya ba da umarnin a tura wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar don gudanar da bincike mai kyau da kuma yiwuwar kama sauran masu laifin.