fbpx
Sunday, February 28
Shadow

An kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani dan banga a Jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu cikin mummunan kisan wani dan banga a karamar hukumar Bebeji da ke jihar.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairu, ya ce masu laifin sun kashe Ibrahim Shuaib kuma sun yi awon gaba da baburarsa, wayoyinsa, da kuma kuɗi.

A ranar 29/01/2021 wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka je Kauyen Gidan Diraman, Kwanar Dangora, karamar hukumar Bebeji, jihar Kano suka kashe wani dan banga, mai suna Ibrahim Shuaib, sannan suka tafi da babura 2 da basu da rajista, wayoyin hannu guda biyu (2) da kuma makudan kudin da ba a tantance yawansu ba, ”in ji DSP Kiyawa.

Bayan samun wannan korafin, kwamishinan ‘yan sanda mai barin gado na jihar Kano, AIG Habu A. Sani, ya gabatar tare da umartar tawagar Operation Puff Adder karkashin jagorancin DSP Shehu Dahiru da su kamo masu laifin.

Nan take tawagar ta shiga aiki kuma a ranar 04/01/2021, watau kwanaki 6 bayan faruwar lamarin, sun kama wani Abdulganiyu Gambo mai shekaru 25, da ke kauyen Kariya, karamar hukumar Kiru, Kano da kuma Mohammed Sani, mai shekaru 28, na Hayin Gwarmai, Bebeji LGA, Kano.

A yayin gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki tare da wasu mutum hudu, sun kashe dan banga tare da kwace kadarorin da muka lissafa a sama.

A halin yanzu ana kan gudanar da bincike don cafke sauran mambobin kungiyar kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *