Lamarin ya farune a karamar hukumar Yawuri dake jihar inda jami’an hukumar tsaro ta NSCDC ta kama wadanda ake zargin.
Kakakin hukumar a jihar, Akeem Adeyemi ya tabbatar da faruwa lamarin.
An kai yarinyar Asibiti inda likita ya tabbatar da an yi lalata da ita har ta dubura.
Kamfanin dillancin labaran Najariya, NAN yace za’a yiwa wadanda ake zargin hukunci bayan kammala bincike.