fbpx
Sunday, February 28
Shadow

An kama wasu shahararrun masu laifi biyu a kan hanyarsu ta fasa bututun mai a Jihar Edo

Jami’an sashin yaki da satar mutane da aikata laifuka ta intanet na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Edo sun cafke wasu shahararrun masu aikata miyagun laifuka biyu a jerin wadanda take nema ruwa a jallo.

Wadanda ake zargin, Samson Ibiweh da Philip Chirer, an kamasu ne a kan titin Ofunama da ke karamar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma a jihar Edo yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa dajin Ofunama don fasa bututun Man Fetur domin basu damar satar kayan da za a sayar.

Ance wadanda ake zargin sun sace bindiga kirar AK49 da alburusai daga jami’an soji da ke aiki a yankin Niger Delta na Najeriya.

Daya daga cikin wadanda ake zargin Samson Ibiweh ya kasance daga kungiyar gungun da suka yi garkuwa da wani shahararren ma’aikacin mai a kan hanyar Siluko da ke cikin garin Benin, jihar Edo.

Harin da suka kai a shekarar 2016 ya yi sanadiyyar rayukan direban ma’aikatar mai.

Hakazalika, wanda ake zargin ya dauki nauyin wata kungiyar ‘yan fashi da makami da suka kai hari tare da yin fashi a kantin sayar da kayan na Etisalat da ke Titin Ibiwe a cikin garin Benin.

A yayin artabun, an raunata wasu mutane, an kuma kwashe miliyoyin nairori, an kame wasu daga cikin wadanda ake zargin tare da gurfanar da su a gaban kotu a shekarar 2016.

Ana sa ran gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan sun kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *