Hukumar ‘yansandan Najeriya data kasa da kasa da kuma hukumar Bincike sun kama wasu ‘yan Najeriya da ake zargi da hannu a wata gagarumar damfarar Yuro Miliyan 14.7.
Kakakin ‘yansandan Najeriya, Frank Mba ya bayyana cewa sun kaddamar da binciken ne bayan da aka aike musu da bukatar hakan daga ofishin Akanta Janar na kasa.
An yi nasarar kama Babatunde Adesanya dan shekaru 50 dake da matakin Digiri na 2, watau Masters, sai kuma Akinpelu Hassan Abbas dan shekaru 41 dake da kamfanin M.D Musterpoint Investment Limited wanda sune da hadin gwiwar wasu ‘yan kasar Holan suka kwaikwayi shafin ILBN Holdings BV dake Holan din inda suka damfari Freiherr Frederick Von han.
Sun yi damfarar ne akan sayen kayan kariya na cutar Coronavirus/COVID-19 wanda aka amince da ciniki kan Yuro Miliyan 14.7, me sayen har ya aika musu Yuro Miliyan 1.5 a matsayin kudin shigar ciniki da kuma wata Yuro 880,000 inda tuni suka kasaftata, saidai bayan da ya ji shiru ba’a kai masa kaya ba, ya tashi zuwa ainahin kamfanin inda suka shaida masa cewa damfararsa aka yi, a nanne sai aka fara bincike.