An kama wata daliba a makarantar sakandare a makaranta da bindiga kirar gida da ake zargin za ta yi amfani da ita wajen harbin malamin ta.
An bayyana cewa yarinyar, daliba ce a Makarantar Sakandare ta Gwamnati a Ikot Ewa, Jihar Kuros Riba, bayan wani malamin ya tilasta mata yanke gashinta mai launi kuma ana zargin ta fusata da hakan.
Bayan haka, sai taje makaranta da bindiga, nan da nan a kayi wa sojoji kiran gaggawa suka kamata tare da bindigar.
A yanzu haka sun tafi da ita domin kara gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya lamarin.