fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

An kama wata Mata a Kaduna data kona Al’aurar ‘yar aikinta me shekaru 14

Jami’an ‘yansanda a Kaduna sun kama wata mata Mrs Yemi Awolola da zargin cin zarafin wata ‘yar aikinta me shekaru 14.

 

Matar ta dauko yarinyarne daga sansanin ‘yan gudun Hijira na Kajuru da Alkawarin zata sakata Makaranta, watanni 15 da suka gabata.

Saidai yarinyar ta bada Labarin cewa matar da ‘ya’yanta cin zarafinta kawai suke, suna tilastamata kwana a bayi da kuma sata shan ruwan bayin da konata da wuta hadda al’aurar ta.

 

Mrs Awolola wadda ma’aikaciyar NNPC ce dai tana hannun jami’an tsaron Kaduna inda kwamishiniyar jin kai da walwala, Hafsat Baba ta tabbatar da cewa zata rubutawa kamfanin da takewa aiki kan wannan cin zarafi sannan kuma za’a tabbatar an hukuntata.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya zata dauki ma'aikata miliyan 1 su yi aikin kidaya

 

Shima dai me magana da yawun ‘yansandan jihar, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.