‘Yansanda a jihar Nasarawa sun bayyana cewa, sun kama ‘yan fashi biyar dake karya da cewa su ‘yansanda ne.
Kakakin ‘yansandan jihar, Rahman Nansel, ne ya bayyana haka inda yace an kama wadanda ake zargin akan hanyar Keffi zuwa Abuja.
Wadanda aka kama sune Aminu Adamu, Adamu Mohammed, Rilwanu Bala, Kabiru Usman, da Bashir A. Bashir.
Yace kwamishinan ‘yansandan jihar ya bayar da umarnin yin binciken kwakwaf akan lamarin.