fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An kara sallamar mutum 10 masu corona a jihar kano bayan da suka warke daga cutar

A ranar Lahadin da ta gabata  jihar Kano ta kara sallamar wasu masu dauke da cutar COVID-19 guda goma wadanda aka tabbatar da warkewar su daga cutar bayan gwaji da akai musu har sau 2.

 

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba shine wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce, marassa lafiyar sun murmure sosai kuma an gwada su basa dauke da cutar a halin yanzu.

 

Sanarwar ta ce jihar ta kuma sami asarar rayuka 3 a ranar Asabar wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga cutar coronavirus zuwa 21.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

 

A karshe ya hori al’umma da suna bin matakan kariya wajan tsaftar hannu da kuma sanya takunkumin rufe hanci don kariya daga cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.