Bisa la’akari da jajircewarsa a tsawon rayuwarsa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma sadaukar da kai da gaskiya, an karrama shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da babbar lambar yabo ta Cibiyar Nazari da bincike kan almundahana ta Nijeriya (CIFCFEN), inda ta gwangwaje shi da lambar yabo kan nagarta da yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaban kwamitin gudanarwa na kwamitin amintattu na CIFCFEN, Dr Iliyasu Gashinbaki, ne ya bai wa shugaban kasa lambar yabo a ranar Talata a Abuja.
Kyautar ita ce babbar lambar yabo ta Cibiyar da aka keɓe ga shugabannin ƙasashen Afirka kawai waɗanda ke da nagarta da halaye nagari.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, shugaban na Nijeriya shi ne shugaban Afrika na farko da aka baiwa kyautar.
Da yake karbar lambar yabon, Shugaba Buhari ya gode wa Cibiyar da ta karrama shi, inda ya ce: ”Wannan karramawa ta kara sanya min fatan cewa a matsayinmu na daidaikun jama’a da ‘yan kasar nan za mu fara rayuwa mai inganci tare da yin ko yi da akidu da ka’idojin wadanda suka kafa wannan kungiya.
Shugaban ya yi alƙawarin duba da kuma amince wa da daftarin doka da ke neman kafa CIFCFEN a hukumance, yana mai cewa kudurin yana gabansa a halin yanzu.
Ya yabawa Cibiyar da ke aiki da kuma yadda ya dace da kokarin hukumomin tabbatar da doka da suka hada da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC) da Hukumar Da’ar ma’aikata (CCB) da kuma ‘Yan sanda.
Ya kuma umurci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su ci gaba da hada hannu da Cibiyar domin amfanin kasa.