fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

An Karrama shugabannin IZALA A Kasar Andulus

Kungiyar Wa’azin Musulunci ta Sautus Sunnah Europe mai rassa a kasashen Turai, ta karrama shugaban kungiyar jama’atu Izalatil bidah wa ikamatissunnah Sheikh Abdullah Bala Lau da Babban Sakataren kungiyar Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe da shaidar (Certificate) na girmamawa Saboda gagarumar nasarorin da suka samu na da’awa da yada Sunnah wanda suka dauki kusan makwanni biyu suna yi a kasashen turai.

Kungiyar mai wa’azin Musulunci ta Sautus sunnah Europe ta karrama Maluman ne a babban Masallacin Juma’a na Masjidul Huda dake birnin Barcelona a Kasar Spain a ranar Laraba bayan kammala Muhadharah wacce manyan  Maluman suka gabatar.
Masoya daga cikin masallacin sun yi cuncirindo suna ta kabbara yayin da ake karrama malamansu.
Allah ya Kara daukaka Malaman Sunnah, ya bada Nasarar Da’awa.
rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya Oladipo Diya ya rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *