fbpx
Friday, July 1
Shadow

An kashe ɗaruruwan ƴan Boko Haram a Tafkin Chadi

Aƙalla mayaƙan Boko Haram 300 aka kashe a yankin Tafkin Chadi a farmakin da dakarun hadin guiwa na rundunar MNJTF suka kai.

Dakarun MNJTF sun ƙunshi na Kamaru Chadi da nijar da Najeriya da Benin.

Jaridar ƙasar Chadi mai zaman kanta ta Tchad Infos ambato kakakin rundunar Kamaudeen Adegoke yana cewa an kashe mayakan na Boko Haram ne a farmaki 30 da aka kai masu a makwannin baya bayan nan.

Ya ƙara da cewa mayaƙa sama da 52,000 da iyalansu suka miƙa wuya ga rundunar MNJTF.

Leave a Reply

Your email address will not be published.