fbpx
Saturday, September 23
Shadow

An kashe mutane 31 cikin awanni 72 a jihohin Inyamurai

Mutane 31 aka kashe a jihohin Ebonyi da Anambra a cikin awannni 72 da suka gabata.

 

A jihar Ebonyi yankunan Effium/Ezza-Effium a Ohaukwu ne suka fi fuskantar matsalar tsaron.

 

Inda aka kashe akalla mutane 26 a jihar.

 

A jihar Anambra ma an kashe mutane da yawa karamar yanda rahoton jaridar Vanguard ya ruwaito.

 

‘Yan Bindiga da ake zargin suna da alaka da kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra na cin karensu ba babbaka inda suke kashe mutanen gari da jami’an tsaro.

 

Lamarin yayi muni ta yanda a har sojoji, ‘yansanda, da jami’an hukumar kiyaye hadurra duk basu tsira ba.

 

Saidai da alama matsalar tsaron yankin ta fara isar al’ummar Inyamurai wanda a yanzu suke ganin wai kamun da gwamnatin tarayya tawa Nnamdi Kanu nenya jawo hakan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *