fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

An kashe mutane biyu, uku sun jikkata a yayin da yan bindiga suka kai hari aa al’ummar jihar filato

Aminiya ta tattaro cewa harin ya afku ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Laraba, inda ‘yan bindigar suka far wa unguwar a kan babura.

Wata majiya ta bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa da su Dalyop Jugu da Yakubu Bot da wadanda suka tsere da raunukan su ne Dahol Jam da Samson Boyi da kuma Badung Boyi.

Jami’an sashin Barkin Ladi na rundunar ‘yan sandan Najeriya ne suka kai wadanda suka jikkata asibiti.

Da yake tabbatar da harin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ACP Gabriel Uba Agaba, ya ce, “Rundunar ta na sane. Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ba sun kashe mutane biyu tare da jikkata wasu biyu a kauyen Rantis na Barkin Ladi.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *