fbpx
Saturday, November 28
Shadow

An Kashe Mutane Hudu, Wasu Sun Ji Rauni Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hare-Haren Kan Al’ummar Jihar Zamfara

Mutum hudu sun rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata a wani hari da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka kai kan kauyen Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis da rana.
A cewar Shehu, lokacin da suka karbi rahoton, wasu daga cikin jami’an da DPO a Maradun ya jagoranta sun amsa kiran da aka yi musu sannan suka isa kauyen don kare sake afkawa kauyukan da ke makwabtaka da su.
“Yan fashin sun gudu kafin isowar jami’an tsaro na hadin gwiwa. Abun takaici, yan fashin sun kashe mutane hudu yayin da wasu uku suka jikkata. Wadanda lamarin ya rutsa da su a yanzu haka suna karbar magani a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gusau, ”.
Hakanan an lura cewa yanzu an tsaurara matakan tsaro a yankin.
A halin yanzu, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Usman Nagogo, ya ba da umarnin gudanar da bincike tare da kame wadanda suka kai harin nan take.
Ya yi ta’aziya ga iyalai, gwamnati da mutanen kirki na jihar game da kisan ba gaira ba dalili kuma ya yi alkawarin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *