Rahotanni sun bayyana cewa, Mutane akalla 113 ne aka kashe a Najeriya a makon da ya gabata.
A satin dake gaban wanda ya gabata kuwa, mutane 48 ne aka kashe a kasarnan.
Na farko shine wanda aka kashe mutane kusan 40 a Owo dake jihar Ondo.
Sai kuma mutane 6 da aka kashe a unguwar Sabo da Hausawa ke ciki a jihar ta Ondo Wanda na zuwane a matsayin harin daukar fansa.
A jihar Sokoto kuwa, mutane da dama ne aka kashe a garuruwan Gebe da Alkammu.
Sai kuma a Kaduna an kashe mutane 32, kamar yanda Premium times ta ruwaito.
A jihar Kwara kuwa, mutane 2 ne aka kashe.
A babban birnin tarayya, Abuja kuwa an kashe wani manomi aka tafi da dabbobinsa.