fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An kashe mutum daya tare da jikkata wasu a yayin arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Yobe

Mutum daya ya rasa ransa yayin da da dama suka samu raunuka sakamakon wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a Garin Mallam da ke karamar hukumar Jakusko ta jihar Yobe.

 

Duk da cewa har yanzu hukumomin ‘yan sanda a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, wani ganau, Musa Amshi, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar.

 

A cewarsa, “lamarin ya faro ne lokacin da wani bafulatani makiyayi ya kutsa kai cikin gonar da ba a girbe ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.