‘Yan Bindiga sun kashe shugaban wani kauye da mutane 14 a jihar Kaduna a wani sabon hari da suka kai jihar.
Lamarin ya farune a Kakura dake karamar hukumar Chukun ranar Lahadi inda hakan ya jefa mutane da yawa cikin tashin hankali.
An kashe shugaban kauyen Isiaku Madaki da wasu mutane 14 a harin da ake tunanin na ramuwar gayyane.
Yawancin mazauna garin Kakura kabilar Gbagi ne. Ranar Asabar ne aka nada Isiaku Madaki shugabancin kauyen inda a ranar Lahadi kuma, wasu da ba’a san ko su wanene ba suka kasheshi.
Hakan yasa aka kaiwa wani garin Fulani hari dan daukar fansa inda a canne aka kashe karin mutane 14n.
Zuwa yanzu dai hukumomin jihar dana ‘yansanda basu ce komai ba akan lamarin.