fbpx
Thursday, July 7
Shadow

An kashe sojoji 2 da dansanda 1 a jihar Abia

Rahotanni daga jihar Abia na cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kashe sojoji 2 dake 14 Bridge, Ohafia.

 

Lamarin ya farune ranar Lahadin data gabata a Owaza dake Ukwa West a jihar Abia.

Hakanan shima wani dansandan Najeriya ya rasa ransa bayan da wasu gungun ‘yan Bindiga suka kaiwa wani shingen ‘yansanda hari a garin Aba.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da hatin inda yace an kashe 2 daga cikin maharan tare da kama mutum 1 sannan maharan sun tsere da bindigar dansandan da suka kashe, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Karanta wannan  Hakika munyi babban rashi, cewar shugaba Muhammadu Buhari bayan rasuwar Muhammad Barkindo

 

Kwamishinan yada labarai na jihar, John Okiyi ya bayyana cewa gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu ya bada umarnin kamo wanda suka aikata wannan aika-aika da kuma kwato bindigar dansandan da suka sace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.