fbpx
Saturday, December 3
Shadow

An kashe wasu makiyaya biyu a wani sabon harin da aka kai jihar Filato

An kashe wasu Fulani makiyaya biyu a yammacin ranar Laraba da yamma, yayin da wasu suka jikkata a wasu hare-hare a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Hakan na zuwa ne bayan da makiyayan suka zargi mazauna yankin Rigwe da sanya wa shanunsu guba, inda daga bisani suka zargi Fulani a yankin da kashe wasu ‘yan asalin kauyuka biyar a karamar hukumar Bassa ta jihar a ranar Talata 29 ga watan Maris.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar a yanzu ya yi zargin cewa ‘yan kabilar Rigwe sun kashe wasu Fulani makiyaya biyu, ya kara da cewa an tsinto gawarwakin wadanda suka mutu tare da jami’an tsaro da suka hada da DCO Jos ta Kudu da sojoji na Operation Safe Haven (OPSH).

Mai magana da yawun kabilar Rigwe, Davidson Malison ya musanta zargin, yana mai bayyana shi a matsayin labari mara tushe kuma marar asali.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *