fbpx
Monday, March 1
Shadow

An kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Filato

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Filato, a ranar Litinin, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne a garin Gindiri, da ke karamar hukumar Mangu, ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) ASP Ubah Ogaba, a cikin wata sanarwa, ya ce an kashe wadanda ake zargin ne bayan artabu da‘ yan sanda a ranar Litinin da rana.
Ya bayyana cewa sauran mambobin kungiyar sun tsere da raunuka daban-daban.
“Tawagar sintiri na Hawk-Eyed na rundunar da ke haɗe da sashinmu na Mangu, a yau da misalin ƙarfe 1 na rana. Sun afkawa masu garkuwar, sunyi masuyar wuta tare da kashe biyu daga cikinsu.
“Sauran mambobin kungiyar sun tsere da raunuka daban-daban na raunin harsasai,” in ji shi.
Ogaba ya ce an kubutar da mutanen biyu da aka yi garkuwar da su ba tare da jin rauni ba kuma an sake hade su da danginsu.
Ya ba da tabbacin cewa an zage damtse don gano sauran ‘yan kungiyar.
PPRO ya kuma yi kira ga jama’a da su bada bayanai masu amfani kan inda ragowar masu aikata laifin suke don kamu su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *