Fiye da mayakan ISWAP 70 ne aka kashe a cikin wani harin jirgin sama a yankin tafkin Chadi, kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jiragen sama daga Najeriya da Jamhuriyar Nijar ne suka kai wannan hare-haren kan yan ta’addan.
Kakakin rundunar sojin sama, Edward Gabkwet, ya ce sun kai hare-hare ta sama a ranar 14 ga watan Afrilu a Tumbun Rego da wani sansanin horaswa da ke kusa, inda suka yi amfani da jiragen sama daga Najeriya da Nijar.