Rahotanni daga Hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua na cewa an kashe ‘yansandan Najeriya 4 tare da sace guda 1.
Kakakin ‘Yansandan Najeriya, Frank Mba ne ya bayyana haka inda yace ya farune a harin kwantan bauna.
Yace Jimullar ‘yansanda 16 ne aka kaiwa harin inda aka kashe 4 amma sauran sun murkushe harin saidai maharan sun tafi da dansanda 1. Yake IGP Muhammad Adamu ya jinjinawa ‘yansandan bisa halin jajircewa da suka nuna sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wanda suka mutu inda yace mutuwarsu ba zata zama a banza ba.