Kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta yi zargin cewa an kashe mata makiyaya 4 da sace shanu 60 a jihar Anambra.
Tace lamarin ya farune a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar na yankin kudun Allahaji Gidado Sidikki ne ya bayyana haka a Awka ga manema labarai.
Yace harin ya farune a wata rugar Fulani dake yankin Ndukwenu, na karamar hukumar Orumba North a jihar ta Anambra.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu ya bayyana cewa zuwa yanzu bai samu rahoto kan lamarin ba amma idan ya samu zai sanar da manema labarai na Daily Trust.