fbpx
Thursday, May 19
Shadow

An kera jirgin sama mafi girma a Duniya: Girman fiffikenshi yafi girman filin kwallon kafa

Wannan hoton jirgin sama mafi girma a Duniya kenan, wanda Paul Allen, wanda aka kirkiri kamfanin Microsoft tare dashi ya kera, ya sakawa jirgin suna Stratolaunch, girman fiifiken jirgin yafi girman filin kwallon kafa.

Shidai wannan jirgin ba’a yishi dan daukar fasinjaba, an yishine dan ya rika harba tauraron dan Adam sararin samaniya daga sama, watau zai dauki tauraron ya tashi dashi sama sannan ya harbashi sararin samaniya, maimakon yanda akeyi yanzu, na harba tauraron dan Adam din daga doron kasa.
Amfanin yin hakan shine, za’a rage yawan gurbatar muhalli da harba tauraron dan Adam din ke haifarwa yayin da aka harbashi daga doron kasa. Haka kuma za’a rage yawan shan man da tauraron dan Adam din keyi idan an harbashi zuwa sama.
Shidai wannan jirgi an fiddoshine domin yin gwaji, bai fara aiki ba tukuna, sai shekarar 2019 ake saran zai fara aiki, ya fito yasha mai kuma ayi gwajin sitiyari da birki da sauran abubuwan dake aiki a jikinshi.
Kafin a kera Stratolaunch, wannan jirgin da ake ganin hotonshi a sama, shine jirgi mafi girma a Duniya, wanda aka kera a shekarar 1947.
Telegraph.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Suna jima'i damu kamar dawaki, kuma suna shan miyagun kwayoyi sosai>>Wata Tsohuwar matar 'yan Boko Haram

Leave a Reply

Your email address will not be published.