fbpx
Friday, February 26
Shadow

An Kona Masallaci A Garin Billiri Dake Jihar Gombe

Rikicin Sarauta a tsakanin kabilar Tangale dake garin Billiri jihar Gomhe ya fara juyewa zuwa rikicin addini.

 

Kwanakin baya Sarkin Tangale wanda ba Musulmi ba ya mutu, yanzu kuma wanda Gwamnatin jihar Gombe ta zaba ya maye gurbinsa Musulmi ne kasancewar ya gaji Sarautar, sai wadanda ba Musulmi ba suka ki amincewa duk da kabilarsu daya.

 

Rikicin nasu na Sarauta yana neman sauya salo zuwa rikicin addini, domin har an kona Masallaci a garin Billiri a jiya.

Menene laifin Masallaci akan rikicin Sarauta da za’a konashi?

 

Hakika wadanda suka kona Masallacin ba su nemi zaman lafiya ba, ya kamata hukuma ta zakulosu don su fuskanci hukunci.

 

Muna fatan Allah Ya kawo zaman lafiya a garin Billiri.

Rariya

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *