Lamarin ya farune ranar Alhamis a Jakande Estate.
Dan Achaban yayi aron hannune inda ya fadawa mutumin dake gefen titi kuma sanadiyyar hakan ya mutu.
Matasa sun taru suka fara Zanga-Zanga sannan suka kama dan achabar da niyyar kasheshi amma jami’an tsaro suka kubutar dashi.
Daga nan ne matasan suka farwa mashinan ‘yan achaba suka kona guda 30.