fbpx
Friday, July 1
Shadow

An kubutar da mahaifiyar dan takarar sanata na jihar Kano daga hannun ‘yan Bindiga

Mahaifiyar dan takarar sanatan jihar Kano, Abdulsalam Abdulkarim A.A Zaura ta kubuta daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka sace ta.

 

Ranar Litinin da safe ne dai aka kama mahaifiyar dan takarar me suna Hajiya Laure Mai Kunu a garin Zaura dake karamar hukumar Ungwaggo ta jihar Kano.

Wanda suka sace ta sun kira waya inda suka ce suna Katsina, saidai Kwana daya bayan sace ta, shugaban karamar hukumar, Abdullahi Garba Ramat ya sanar da cewa, an kubutar da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published.