Tuesday, December 3
Shadow

An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

Garin Aba ya rikice inda sojoji suka mamayeshi bayan kisan abokan aikinsu 5.

Wasu da ake kira da ‘yan Bindigar da ba’a san ko su wanene ba amma ana kyautata zaton ‘yan IPOB ne kawai da suke fakewa da wannan sunan suka yi kisan.

Sun yi kisanne ranar Laraba bayan sun tursasa kowa ya je gida ya zauna dan tunawa da mutanen da suka mutu a yakin Biafra.

Lamarin yasa hukumar sojojin Najeriya ta sha Alwashin sai ta rama wannan kisa da kakkausar murya.

Rahoton jaridar Vanguard yace sojojin sun shiga kasuwanni suka tursasa mutane suka kulle shaguna da kuma a jiya, Juma’a yawanci yara basu je makaranta ba a garin.

Karanta Wannan  Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba'a gano inda take ba

Hakanan an ga jirage masu saukar Angulu suna shawagi a sararin samaniyar wajan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *