fbpx
Thursday, August 11
Shadow

An kulle makarantun Islamiya 2 a Kaduna saboda zargin dirkawa daliba ciki

Gwamnatin Kaduna ta rufe makarantun Islamiyya 2 bisa yin fyaɗe da ciki

Hukumar Kula da Ingancin Makarantu ta Jihar Kaduna, KSSQA ta rufe wasu makarantun Islamiyya guda biyu a yau Juma’a sakamakon zargin yi wa ɗaliba ƴar shekara 6 fyaɗe da kuma yi wa ɗaliba ƴar shekara 12 ciki.

Ɗaya daga cikin makarantun, Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an, located a Rigasa, an rufe ta ne sakamakon yi wa ɗaliba ƴar shekara 6 fyaɗe.

Ɗaya makarantar da ba a baiyana sunan ta ba amma an tabbatarwa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa NAN cewa a Tsohon Masallacin Juma’a na Kachia, Ƙaramar Hukumar Kachia ta ke, inda wani malami ɗan shekara 50 ya yi wa ɗaliba ƴar shekara 12 ciki.

Shugaban KSSQA, Idris Aliyu ya baiyana cewa an yiwa yar shekara 6 fyaɗe a makarantar da ke rigasa amma sai shugabannin makarantar su ka rufe maganar, ta in da su ka nuna ba su san da lamarin ba.

Aliyu ya ƙara da cewa a bayanan da Hukumar Ilimi ta Kaduna ta samu, kakar yarinya ta je ta yi korafi a kan abinda ya faru ga shugabannin makarantar amma sai a ka ce ɗalibai da malamai sun mata duka.

Karanta wannan  Tinubu zai cigaba da gina Najeriya kamar yadda shugaba Buhari yayi, cewar kungiyar yakin neman zabensa

Ya ƙara da cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada umarnin rufe makarantun na sai-baba-ta-gani har sai an kammala bincike an kuma samu waɗanda su ka aikata.

Ya ce za a rike Shugaban makarantar har sai an samu wanda ya yiwa yarinyar fyaɗe ko ita da kanta ta gane shi.

“Haka kuma wadanda su ka yiwa kakarta duka suna za a kai su kotu,”

Amma kuma shugaban makarantar ya musanta batun fyaɗe in da ya ce ba fyade bane, “kawai dai wani ne ya jiwa yarinyar rauni da ice a gaban ta.

A halin yanzu dai ƴan sanda na ci gaba da bincike a kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.