fbpx
Saturday, August 20
Shadow

An kwana 40 da sace wannan yarinyar a Kano

INA AKA KWANA DA BATUN SACE HANIFA?

Kwanaki 40 Kenann Da Sace Ta A Birnin Kano

Daga Kamal A. Rufa’i Rawaiya

Yau kimanin kwanaki arba’in da wasu da ba a san ko su waye ba suka sace wata yarinya mai shekara biyar a birnin Kano.

Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a unguwar Kawaji bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma Adaidaita-Sahu.

Wani kawun Hanifa ya shaida wa manema labarai cewa mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce “ɓarayin sun zo ne a Adaidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida. Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita.”

Karanta wannan  So makaho ne: Wata matashiya 'yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin sahibinta mai dauke da cutar kanjamau

Birnin Kano ya sha fuskantar sace-sacen ƙananan yara a ƴan shekarun nan, abin da ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa kwamatin bincike domin ganowa da kuma bin haƙƙin yaran da ake sacewa.

A Oktoban 2019, rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu da ake zargin sacewa da kuma safarar yara ‘yan asalin jihar zuwa garin Onitsha na Jihar Anambra da ke kudancin ƙasar, inda ake tilasta musu sauya addini da al’ada.

Allah Yasa Masu Ire-Iren Wannan Aika-Aika Su daina

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.