fbpx
Thursday, June 30
Shadow

An kwantar da mutane 201 a jihar Kano bayan sun shaki Kemikal

Lamarin ya farune a unguwar Sharada dake kanon, jiya Juma’a.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN yace ‘yan gwagwan ne suka fasa tukwanen dake dauke da gasdin wanda ya shiga gidajen Al’umma.

 

Wasu mutanen an kaisu Asibitin Murtala inda aka kai wasu Asibitin Jaen.

 

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA reshen jihar Kano, Nuradeen Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Jami’in Asibitin Murtala, Hussaini Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace cikin mutane sama da 70 da aka kai Asibitin su, 65 sun dawo cikin hayyacinsu.

Karanta wannan  Gwamnatin Najeriya ta ɗau lauyoyi domin tsayawa Ekweremadu

 

Ministar kula da jin kai da ibtila’i, Sadiya Umar Farouk ta samu wakilci a wajan diba wanda abin ya shafa. Ta basu tabbacin cewa zata tallafa musu kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.