fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

An kwantar da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz asibiti 

An kwantar da Sarkin Saudiyya kuma mai kula da masallatai biyu masu tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz a asibiti a birnin Jeddah da ke gabar tekun Bahar Maliya domin duba lafiyarsa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata domin dakile cece-kuce kan lafiyar sarkin mai shekaru 86 da haihuwa.

A cewar rahoton na Masarautar, Sarkin ya shiga asibitin kwararru na Sarki Faisal da ke birnin Jeddah da ke gabar teku a ranar Asabar “don gudanar da wasu gwaje-gwajen lafiyarsa.”

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Yan ta'adda sun kaiwa jirgin kasan yakin neman zaben gwamnan jihar Osun hari

Sarki Salman bn Abdulaziz ya zama sarki na bakwai kuma mai mulkin babban mai fitar da man fetur kuma mafi girman tattalin arzikin kasashen Larabawa a shekarar 2015 bayan rasuwar mai kula da masallatai biyu masu alfarma Sarki Abdullah bin Abdulaziz.

Kotun masarautar Saudiyya ta yi addu’ar Allah ya ba Sarkin lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.