fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

An kwantar da tsohon shugaban Mali Keita a asibiti

Rahotanni daga Mali na cewa an kwantar da hambararren shugaban kasar a asibiti.

Kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya ambato majiyoyi biyu daga asibiti na cewa tsohon shugaban kasar yana samun kulawa.

An hambarar da Ibrahim Boubakar Keita mai shekara 75 daga kan mulki ne makonni biyu da suka wuce sannan kuma aka tsare shi na tsawon kwana goma a wani sansanin soji kafin a ba shi damar walwala.

Lokacin da ake gudanar da tattaunawar sulhu, Mr Keita ya ce ba ya son komawa kan mulki.

Karanta wannan  Na So A Ce Ana Kai Ziyara Lahira, Da Na Ziyarce Ki, Cewar Matashin Da Budurwar Sa Ta Rasu Ana Dab Da Aurensu

‘Yan hamayya sun kwashe watanni suna kira a gare shi ya sauka daga mulki, inda suka dora alhakin tabarbarewar tattalin arziki da tsaro, da kuma cin hanci da rashawa a kansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.