Rahotanni sun bayyana cewa mahaifiyar Yusuf Buhari, matar shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari na can Asibitin da aka kwantar da dan nata itama an bata gado, kafar watsa labarai ta daily Post ta bayyana cewa an kwantar da Hajiya A’isha Buhari a yammacin jiya, Alhamis, damuwar halin da danta yake cikine yasa har saida aka bata gado a Asibitin.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Amma halin da take cikin bawai yayi tsanani neba.
Haka kuma Daily Post ta ruwaito cewa manyan ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa sunje gaishe da Yusuf Burin a Asibitin.
Muna fatan Allah ya basu lafiya da sauran al’umma baki daya.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});