Kungiyar SERAP dake saka ido kan yanda ake gudanar da ayyukan gwamnati ta maka shugaban kasa, Muhammadu Buhari a kotu kan yafewa tsaffin gwamnonin Filato dana Taraba, watau Joshua Dariye da Jolly Nyame kan daurin da aka musu na satar dukiyar gwamnati.
Kungiyar na neman kotu data soke wannan afuwa da shugaba Buhari yawa wadannan tsaffin gwamnoni.
Shugaba Buhari ya yafewa wadannan gwamnoni da kuma wasu masu laifi 157 dake daure a gidan yari.
An daure gwamna Dariye bisa laifin satar Biliyan 1.16 yayin da aka daure gwamna Nyame kan satar Biliyan 1.6.
Kungiyar tace yafewa wadannan tsaffin gwamnonin zai baiwa sauran manyan ‘yan siyasa damar yin irij abinda suka yi.