fbpx
Sunday, August 7
Shadow

An maka wani makiyayin da yayi garkuwa da matar aure yayi lalata da ita a jihar Kwar

Hukumar ‘yan sandan Najerya ta jihar Kwara ta maka wani makiyayin da yayi garkuwa da wata mata yayi mata fyade a kotun magistare.

Korun ta caji makiyayin mai suna da Hassan Namusa dan shekara 25 da laifuka biyu ne, na garkuwa da mutane da kuma fyade.

Inda hukumar ‘yan sanda ta cewa kotun Namusa yaga matan ne guda biyu sun debo ruwa a rafi, Hauwa da Hurewa matan Alh Shehu Sanni.

Sai ya bar Hurewa saboda yaron dake bayanta amma ya tafi da Hauwa yayi lalata da ita, saboda haka hukumar take rokar kotun data hukunta shi don laifinsa yafi karfin beli.

Karanta wannan  Rundumar sojin sama sun hallaka shugaban 'yan ta'addan Boko Haram da tawagarsa a jihar Maiduguri

Kotun ta daga shari’ar izuwa ranar 14 ga watan Yuli.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.