Tsohon kakakin majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki yace sai da aka masa barazanar tsigewa daga kujerarsa saboda yace kada Gwamnatin Buhari ta ciwo bashi.
Saraki ya bayyana cewa, yana da kwarewar da zai mulki Najeriya, ya bayyana hakane a wajan ganawar da yayi da wakilan PDP a Calabar.
Saraki yace idan aka bashi dama zai maida Najeriya kan turba.
Saraki yayi gargadin cewa, Najeriya ta kama hanyar lalacewa.