fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An Nada Sabon Kwamitin Rikon Kwarya na Jam’iyyar APC: Ga dukkan Alamu an rufe shafin Adams Oshiomhole

An nada gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC.
Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar ne ya dauki wannan mataki bayan da ya soke kwamitin rikon APC din a wani taro da ya gudanar a ranar Alhamis da rana.
Hakan ya biyo bayan shawarwarin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar ne, kamar yadda mai taimaka masa kan shufakan sada zumunta Bashir Ahmed ya fada a shafinsa na Twitter.
Jam’iyyar APC dai na ta fuskantar matsaloli a baya-bayan da suka shafi shugabancinta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Gadon Boko Haram mukayi a wurin PDP kuma kuma yanzu mun kusan babu su a doron kasa duk mun hallaksu, cewar gwamnatin tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published.