fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An nada tsohon Sarkin Kano:Muhammad Sanusi II, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

An nada tsohon Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniya a Najeriya

An naɗa tsohon sarkin Kano Sanusi na II a matsayin jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.

Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoraci naɗa tsohon sarkin a matsayin Khalifa a babban taron ɗariƙar da aka gudanar a jihar Sakkwato.

Sarki Sanusi na II yanzu ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya.

Tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu ba a naɗa sabon Khalifa ba a Najeriya.

Taron ya samu halartar manyan shugabannin ɗarikar Tijjaniya na Najeriya da wajen ƙasar da suka haɗa babban malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.