fbpx
Sunday, June 26
Shadow

An sace fasinjoji da dama yayin da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka kai hari a Borno

A ranar Litinin 6 ga watan Yuni ne wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai hari kauyen Lawan Mainari da ke kusa da Mainok kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Borno.

Channels TV ta rawaito cewa ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da fasinjoji da dama a yayin da suka kona motoci tara, ciki hadda manyan motoci masu jigilar kayan abinci, a yayin harin da aka kai a wata al’umma da ke da tazarar kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Karanta wannan  "Kiran da aka yiwa gwmnati ta soke kungiyar malamai ta ASUU shirme ce">>Malamin jami'ar Port Hacourt

Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito cewa, duk da cewa hukumomi ba su ce uffan ba kan lamarin, amma da yawan masu ababen hawa da ke bin hanyar sai da suka jira a kauyukan da ke kusa, ko kuma su koma Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.