fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An sace fiye da dalibai 1,500 a Najeriya>>Amnesty International

Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin da Adam ta Amnesty International ta ce shekara takwas bayan da kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan matan makarantar Chibok 276, fiye da dalibai 1,500 wasu kungiyoyi suka sace, kuma hukumomin kasar sun kasa kare su.

Amnesty International ta bayyana haka ne cikin wani rahoto da ta fitar a shafinta.

Rahoton kungiyar ya ce a cikin dalibai 276 na Chibok da aka sace, an kashe 16 kuma har yau ba a san inda 109 suke ba.

Sannan a dalilin sace daliban da ake yi an sun kulle makarantu masu yawa kuma an fara yi wa dalibai mata auren wuri.

Amnesty ta kuma ce an sace dalibai 1,500 cikin wata 22 ne, kuma har zuwa wannan lokacin akwai dalibai kimanin 120 da ke hannun wadanda suka sace su.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Rundunar soji ta damke 'yan bindigar da suka kashe mutane 40 a cocin katolika ta jihar Ondo

Cikin dalibai 102 da aka sace a makarantar gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri, har yanzu tara na hannun masu garkuwa da su, haka kuma ba a sako daya daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist High School ta Kaduna cikin dalibai 121 da aka sace ba.

Sannan an kashe dalibai biyar na jami’ar Greenfield ta Kaduna, kuma wani dalibin makarantar sakandaren Kankara ma ya rasa ransa.

Akwai kuma dalibai biyar na makarantar Islamiyar Salihu Tanko da ke Tegina da masu garkuwa da su suka kashe, inda a karshe rahoton ya bayyana cewa daliba Leah Sharibu ta makarantar gwamnati da ke Dapchi ce kadai ba a sako ba cikin dalibai 276 da aka sace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.