fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An sace mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng a jihar Adamawa

An sace mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng na jihar Adamawa, Kama Bakta.

Wani jami’in karamar hukumar ya ce an sace Bakta ne a safiyar ranar Talata a garinsu, Bakta.
“Abin bakin ciki, an sace mataimakin a yau misalin karfe 1:20 na 16 ga watan Yuni 2020 wannan bakar rana ce. Hon.Kama Lazarus BaktaMataimakin shugaban karamar hukumar shelleng, ”majiyar ta fada a cikin wani sako ga manema labarai.
Wani mazaunin yankin ya ce, “masu satar sun shigo da yawansu dauke da bindigogi sannan suka shiga gidan dan siyasa da misalin karfe 2 na safe a ranar Talata.”
“Sun ta harbi cikin iska don shelanta isowarsu kuma nan da nan suka shiga suka dauke dan siyasan.
“Duk abin ya kasance mai ban tsoro kamar yadda babu wanda ya iya samun karfin gwiwa don kalubalanci masu satar mutanen da ke shirye su kashe duk wanda ya tunkare su”.
Yanzu haka mutanan garin suna cikin wani hali, saboda idan mataimakin shugaban bai tsira ba, to wane ne ya tsira ”in ji mazaunin, wanda ke da kusancin da Dan siyasan.
Da yake tabbatar da satar, Kakakin yan sanda a jihar, Sulaiman Nguroje, ya ce yan sanda sun tattara mafarautan yankin kuma a yanzu haka suna kan hanyar da masu satar mutanen suka bi.
“Zan iya tabbatar muku cewa ‘yan sanda da mafarautan yankin sun hadu kuma suna kan hanyar masu satar. Za mu yi iya kokarinmu har sai an sako wanda aka sace sannan kuma a gurfanar da wadanda suka aikata lamarin a gaban kuliya, ”in ji mataimakin Sufetan yan sanda.
Sata don fansa ya zama ruwan dare a Adamawa da sauran sassan Najeriya, kamar yadda sauran nau’ikan laifuka kamar hare-haren ‘yan bindiga da tashe tashen hankula acikin al’ummomi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Yadda hukumar 'yan sanda ta ceto wani dan daudu a hannun matasa da sukayi masa taron dangi zasu kashe shi a jihar Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published.