fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An sace motar da aka baiwa bakanike gyara yana tsaka da lalata da karuwa a Otal

Wani bakanike a jihar Nasarawa, John Simon ya fada taskun barayin mota bayan da ya je da motar da aka bashi gyara wani Otal.

 

John ya kammala gyaran motar da aka bashi inda ya dauke ta dan kaiwa me gidansa a Abuja, saidai akan hanya sai ya tsaya a wani otal inda ya shiga daki da wata karuwa Stella Emeerga, yana can aka sace motar, saidai tashi yayi da safe yaga wayam.

Ya kaiwa ‘yan sanda kara inda aka hada dashi da karuwar da wani da ake zargi aka kulle. Bayan tsawon lokaci ba tare da gano motar ba, me motar wanda dillancin mota yake ya kaiwa shugaban ‘yansandan Najeriya korafi inda kuma aka mayar da binciken sashen bincike na musamman na ‘yansanda.

 

Daga baya dai dayan wanda ake zargi da aka kama, Sunday Francis ya amsa laifinsa inda yace shi da wani abokinsa da karuwar ne suka shirya satar.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

 

Saidai yace wanda aka sayarwa da motar ya tsere. Ya kara da cewa bakaniken yayi mankas da giya lokacon da suka shiga dakin suka dauki makullin motar ba tare da ya sani ba.

 

Saidai ita karuwar ta musanta haka inda tace bata hada kai dasu ba kawai dai daya daga ciki ya kwankwasa mata daki da dare suka fita neman ruwa.

 

Shima direban ya bayyana cewa ya ganta dai ta fita daga dakin amma daga baya ta dawo suka yi lalatar amma bai dauka akwai wani abuba sai da safe kawai da ya tashi ya ga ba mota.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.