Mahara a jihar Nasarawa sun sace matar shugaban matasan kabilar Eggon, Daniel Anyabuga. Lamarin ya farune a a daren jiya, Talata kamar yanda Rahotanni suka bayyana.
Maharan da suka kai 10 sun shiga gidan na shugaban Eggon da misalin karfe 10 zuwa 11 na dare inda suka dauki matar suka tafi da ita.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama mutane 4 sannan kuma mashinan aka yi amfani dasu wajan harin suma an kamasu.
Ya kuma yi kira ga mutane da su bada hadin kai wajan samar da bayanan da zasu kai gakama wanda suka yi wannan danyen aiki.