fbpx
Thursday, August 11
Shadow

An sace yara huɗu da mahaifiyarsu a Kaduna

Ƴan bindiga sun sace wata mata da ƴayanta huɗu a wani ƙauye da ke kusa da Sabon Tasha da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ne a lokaci guda da wani yunƙurin yin garkuwa da mutane duk a Unguwar Sabon Tasha.

Ya ce maharan waɗanda sun kai 30, wasunsu na sanye da kayan sojoji ɗauke da muggan makamai inda suka yi ƙoƙarin shiga wani gida a GRA Sabon Tasha amma jami’an tsaro sun daƙile hakan sai dai sun shiga wani ƙauye sun sace wata mata da ƴaƴanta huɗu.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada sabuwar mai bashi shawara akan harkar siyasa

Ya ce waɗanda aka sace an yi awon gaba da su zuwa wani wurin da ba a sani inda ya ce an ƙoƙarin ceto su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.