fbpx
Friday, May 27
Shadow

An saka dokar hana fita a Sokoto

Gwamnatin Jihar Sokoto ta saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka gudanar a yau Asabar.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce dokar za ta fara aiki nan take.

An ɗauki matakin ne “saboda dawo da doka da oda a birnin Sokoto da jihar baki ɗaya”, a cewar sanarwar.

Masu zanga-zangar na nemanjami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyarda ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).

Leave a Reply

Your email address will not be published.