fbpx
Friday, July 1
Shadow

An saka dokar hana fitar dare a jihar Anambra

Gwamnatin jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya ta saka dokar hana fita a jihar.

Gwamnan jihar Charles Soludo ne ya sanar da dokar a ranar Laraba a jawabin da ya gabatar a kafar talabijin.

Gwamnatin ta hana fita daga 6 na dare zuwa 6 na safe daga ranar Alhamis, kuma dokar ta shafi ƙananan hukumomi guda takwas.

Gwamnatin kuma ta hana yin okada da babur mai kafa uku a kananan hukumomin.

Matakin na zuwa bayan kisan mace mai ciki mai suna Harira Jubril da ƴayanta hudu da ƴan bindiga suka yi wa kisan gilla a ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.